United ta kai zagayen gaba a kofin FA

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United tana ta biyu a kan teburin gasar Premier ta shekarar nan

Manchester United ta yi nasarar cin Huddersfield 2-0 a wasan zagaye na biyar a kofin FA da suka kara a ranar Asabar.

United ta ci kwallayen ta hannun Romelu Lukaku, wanda ya ci na farko a minti na biyar da fara tamaula, sannan ya kara na biyu bayan da aka dawo daga hutu.

Wannan ne wasa na uku da United ta buga da Huddesfield a bana, inda ta ci karawa biyu, Huddersfield ta ci daya.

Huddesfield ce ta fara doke United a wasan farko a gasar Premier da ci 2-1 a ranar 21 ga watan Oktoban 2017, United ta ci 2-0 a Old Trafford a ranar 3 ga watan Fabrairun 2018.

Labarai masu alaka