Damben Shamsu Kanin Emi da Shagon Aleka
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Damben Shamsu Kanin Emi da Shagon Aleka

Dambe 10 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma dake unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Mohammed Abdu ne ya hada wannan rahoton

Cikin wasannin har da wanda Shamsu Kanin Emi daga Arewa ya buge Shagon Aleka daga Kudu a turmin farko.

Damben da ya yi kisa shi ne wanda Shagon Jimama daga Kudu ya doke Garkuwan Sojan Kyallu Guramada a turmin farko, da wanda Shagon Dogon Auta daga Kudu ya buge Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa.

Da wasan da Bahagon Ummarun Gundumi ya buge Nokiyar Dogon Sani daga Arewa.

Sai wasannin da aka tashi canjaras:

  • Shagon Hussaini Na Barkoji da Shagon Ummarun Gundumi Guramada
  • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Bahagon Sama'ila daga Kudu
  • Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Shagon Shamsu daga Arewa
  • Shagon Alhazai daga Arewa da Danladi Na Dutsen Mari Guramada
  • Shagon Bahagon Fandam daga Kudu da Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
  • Shagon Bahagon Fandam daga Kudu da Dogon Washa Guramada

Labarai masu alaka