Kofin FA: Wankin hula ya kai Tottenham dare ta yi 2-2 da Rochdale

Steve Davies lokacin da yake rama ta biyu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Steve Davies ya rama wa Rochdale kungiya ta karshen tebur a gasar League One bal ta biyu a wasan da ta rike wa daya daga cikin na gaba-gaba a Premier Tottenham wuya

Steve Davies ya jika wa Tottenham aiki da bal din da ya rama wa kungiyarsa ta gasar League One, Rochdale a wasan cin kofin FA, zagaye na biyar,suka tashi 2-2, sakamakon da ya sa dole sai sun sake karawa.

Henderson ne ya ci wa Rochdale bal din farko ana shirin tafiya hutun rabin lokaci a minti na 45, sannan bayan an dawo daga hutun ne a minti na 59 Lucas Moura ya rama wa Tottenham.

Sai kuma a minti na 88 Harry Kane ya kara wa Tottenham ta biyu, da bugun fanareti bayan da aka yi wa Dele Alli keta, wadda ita ce bal ta 34, da ya ci wa kungiyar a kakar nan.

Ana dab da tashi ne a cikin mintunan da aka kara bayan 90, na ramakon lokacin da aka bata sai Davies ya yi wa Tottenham barna ya rama wa Rochdale bal ta biyu, aka ta shi 2-2, sakamakon da ya sa dole kungiyoyin su sake haduwa wasa na biyu, a gidan Spurs din.

Rochdale ita ce ta karshen tebur a gasar League One, wadda ita ce gasa ta mataki na uku a Ingila