Jadawalin Kofin FA: Man Utd za ta kara da Brighton

Kociyan Brighton Chris Hughton da na Manchester United Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Brighton ta doke Coventry ta gasar League One 3-1 ranar Asabar, yayin da United ta ci Huddersfield 2-0

Manchester United za ta kara da Brighton a wasan dab da na kusa da karshe na cin kofin FA, kamar yadda kungiyoyin biyu suka yi wasan karshe na cin kofin a shekara ta 1983.

A wancan lokacin Manchester United ta dauki kofin bayan ta doke Brighton 4-0 a wasan da suka sake yi na biyu, kasancewar na farko sun tashi canjaras 2-2.

A jadawalin wasan Southampton za ta je gidan wadda za ta yi nasara a karawar da za a yi ranar Litinin din nan tsakanin Manchester City da Wigan, yayin da Leicester City da Chelsea za su fafata.

Wigan, ta biyu a teburin gasar League One, za ta hadu da Manchester City a ranar Litinin din nan (19:55 GMT).

Yayin da Leicester, da ta ci Sheffield United 1-0 ranar Juma'a, za ta karbi bakuncin Chelsea, wadda ita ma a ranar juma'ar a gidanta ta casa Hull City 4-0.

Idan aka samu gwani bayan karawa ta biyu tsakanin Tottenham da Rochdale, kungiyar da ta yi galaba za ta hadu da Sheffield Wednesday ko Swansea, wadanda su ma za su sake fafatawa kasancewar an kasa samun gwani a wasansu na ranar Asabar da suka yi canjaras ba ci (0-0).

Dukkanin wasannin na matakin dab da na kusa da karshe na cin kofin na FA za a yi su ne a watan Maris mai zuwa daga ranakun 16 zuwa 19.