Kofin FA: Kamfani ya bayar da hakuri kan kwallon Juan Mata

Hoton yadda JUan Mata ya ci kwallon Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Kamfanin ya bayar da hakuri da cewa an yi kuskure ba a yi amfani da hoton da ya dace ba wajen haramta kwallon

Kamfanin na'urar bidiyon da ake amfani da ita mai taimaka wa alkalin wasa wajen warware takaddama (VAR) a wasa ya bayar da hakuri kan abin da ya ce kuskren amfani da hoton da ba shi ne ba, wajen haramta kwallon da Juan Mata ya ci a wasan Man United da Huddersfield na kofin FA.

Kamfanin Hawkeye ya ce an samu kuskure ne wanda ya sa aka sanya wa alkalin wasa hoton da ba shi ne, wanda kuma ya yi amfani da shi wajen yanke hukuncin hana kwallon da cewa dan wasan ya yi satar gida.

A ranar Asabar ne bayan da Mata ya ci wa United bal ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, sai alkalin wasa Kevin Friend ya kasa kunne inda ya ji bayanin da na'urar ta turo masa, kuma bayan jira na kusan minti daya sai ya hana kwallon da cewa Mata ya yi satar gida.

A Ingila ana gwajin amfani da na'urar ne mai taimaka wa alkalin wasa warware takaddama a gasar cin kofin FA da na Carabao a wannan kakar.

An yaba amfani da na'urar bayan da ta haramta bal din da Kelechi Iheanacho ya ci wa Leicester, lokacin da suka doke Fleetwood 2-0, a wasan zagaye na uku na cin kofin FA a watan Janairu.

Amma kuma tsohon kociyan Ingila Alan Shearer ya soki amfani da na'urar bayan da ta kasa ba wa Chelsea fanareti lokacin wasan da suka sake na kofin FA da Norwich.