Guingamp ta dauki dan Didier Drogba wasa

Isaac Drogba Hakkin mallakar hoto GUINGAMP
Image caption Burin Isaac Drogba shi ne ya zama dan wasan tawagar Ingila ta kasa

Dan tsohon dan wasan gaba na Chelsea Didier Drogba mai shekara 17 Isaac ya shiga kungiyar Guingamp ta gasar Ligue 1 ta Faransa.

Isaac Drogba, wanda kamar mahaifin nasa dan wasan gaba ne a da yana taka leda ne a kungiyar matasa ta Chelsea.

Matashin ya koma kungiyar ta Guingamp ne shekara 16 bayan babansa ya tafi kungiyar daga Lens a kan fam 80,000.

Didier Drogba, wanda ya ci kwallo 24 a wasa 50 da ya yi wa Guingamp, ya sanya wata sanarwa a shafinsa na Instagram cewa yana matukar alfahari da dan nasa Isaac Drogba.

Biyu daga cikin tsoffin abokanan wasansa a Chelsea, na daga wadanda suka aika masa da murnarsu da kuma fatan alheri kan wannan matsayi da dan nasa ya kai.

Tsoffin 'yan wasan kuwa su ne Frank Lampard da kuma tsohon kyaftin din Chelsea John Terry.

Didier Drogba ya yi kasa da kaka biyu ne a Guingamp daga nan ya koma Marseille, inda a can kuma ya yi kasa da shekara daya kafin ya koma Chelsea a 2004.

A Chelsea din ne ya ci kofin Premier hudu, da na FA shi ma hudu da kuma na zakarun Turai, tare kuma da yi wa kasarsa Ivory Coast wasa sau 104.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a shekara ta 2015 ya ce dan nasa wanda aka haifa a Faransa yana son ya zama dan wasan tawagar Ingila.