Sergio Aguero ya yi fada da mai goyon bayan Wigan

Magoya bayan Wigan a cikin fili Hakkin mallakar hoto Others
Image caption 'Yan sanda sun ce sun yi kame, bayan kutsen da magoya bayan na Wigan suka yi a fili

Shugaban Wigan David Sharpe ya ce kungiyar za ta yi aiki tare da hukumar kwalllon kafa ta Ingila da 'yan sanda domin nazarin hotunan bidiyon yadda aka yi magoya bayansu suka kutsa tare da mamaye fili a lokacin da suka doke Manchester City 1-0 a ranar Litinin.

A yayin wannan kutse ne dan wasan City Sergio Aguero ya yi sa-in-sa da wani mai goyon baya, inda ya ce mutumin ne ya tofa masa yawu da kuma zaginsa.

Wasu magoya bayan na Wigan, a yayin murnar da ta sa su kutse cikin filin bayan da kungiyar tasu ta fitar da Manchester City a zagaye na biyar na gasar ta cin kofin FA, sun rika yage allunan talla da ke filin suna jefa wa 'yan sanda.

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Ingila FA, ta ce za ta yi nazarin rahoton alkalin wasan da ya jagoranci fafatawar da kuma hotunan bidiyon lamarin.

Wani babban jami'in 'yan sandan Manchester Stuart Ellison ya ce kwallon kafa wasa ne na iyali, kuma duk wani abu na kokarin kawo cikas cikinsa ga 'yan wasa ko kuma 'yan kallo abu ne da ba za a yarda da shi ba.

A wata sanarwa da ya fitar babban jami'in kungiyar ta Wigan Jonathan Jackson ya ce kungiyar ta ji takaicin wannan abu da bai dace ba, wanda wasu 'yan kalilan din magoya bayansu suka yi, kuma za su gudanar da cikakken bincike.

Sakamakon wasan dai ya kawo karshen fatan Manchester City na cin kofuna hudu a kakar nan, wadanda suka hada da na Premier da shi na FA, da na League, wanda aka yi wa lakabi da Carabao a bana da kuma na zakarun Turai.