An tuhumi West Ham kan amfani da abubuwan kara kuzari

Filin wasa na West Ham Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Ana tuhumar West Ham da laifin saba ka'idar da ta shafi dokar amfani da abubuwan kara kuzari

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, ta tuhumi kungiyar West Ham da laifin da ke da nasaba da saba ka'idar amfani da abubuwan kara kuzari.

An zargi kungiyar ta gasar Premier ne wadda a karo uku cikin wata 12 ta kasa tabbatar da ganin bayanan da suka danganci inda 'yan wasanta suke, daidai suke, ba wani sabani ko kuskure.

Kungiyar tana da wa'adin nan da ranar 27 ga watan nan na Fabrairu ta bayar da bahasi kan tuhumar.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta West Ham a wata sanarwa ya ce, matsalar ta shafi harkokin gudawar ne kawai, amma ba wani dan wasa ba.

Hukumar kwallon kafar ta Ingila ba ta fito fili ta bayyana takamaimai irin ka'idar da kungiyar ta saba ba.

A ka'ida dai kowa ce kungiya kan gabatarwa da hukumar kwallon ta Ingila bayanan inda 'yan wasanta suke, domin ta kan kai ziyarar bazata, inda ake yi wa 'yan wasa gwaji na abubuwan kara kuzari da aka haramta amfani da su a wasa.