Zakarun Turai: Barcelona ta rike Chelsea 1-1, Bayern ta casa Besiktas 5-0

Lionel Messi lokacin da ya farke wa Barcelona Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bal din da Lionel Messi ya ci ita ce ta 28 a kakar nan, kuma ta farko a wasa shida na karshe

Lionel Messi ya ci kwallon da ya farke wa Barcelona ta hana Chelsea samun muhimmiyar galaba a wasansu na farko na matakin kungiyoyi 16 na kofin zakarun Turai a Stamford Bridge.

Willian wanda sau biyu yana yi wa Barcelona kararrawa, yana sharara bal tana dokan tirken raga, shi ne ya yi dacen cin bakin a minti na 62.

Sai dai kuma nasarar ta Chelsea ta yi karko ne na minti 13 kawai, kafin Andreas Christensen ya yi kuskuren bayar da wata bal, wadda takwaransa na Barcelonan and Andres Iniesta ya tsinta, kuma bai yi wata-wata ba ya nemi Messi, wanda ya daddage ya kwarara wa Thibaut Courtois, ta kwana a raga.

Kungiyoyin za su yi karawa ta biyu ne a ranar Laraba 14 ga watan Maris a gidan Barcelona, wadda take da dama fiye da Chelsea saboda kwallon da ta zura musu a gida.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bayern ta mamaye wasan da sama da kashi 68 cikin dari a kan Besiktas

A daya wasan na zakarun Turai da aka yi a daren na Talata zakarun Jamus, Bayern Munich ta caskara Besiktas 5-0, bayan da alkalin wasa ya kori dan wasan kungiyar ta Turkiyya, Domagoj Vida a minti na 16.

Wasan shi ne na 14 da Bayern ke ci a jere.