Za mu daure Alexis Sanchez - kociyan Sevilla

Alexis Sanchez a Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alexis Sanchez ya koma Manchester United daga Arsenal a watan Janairu a wata musaya da Henrikh Mkhitaryan

Kociyan Sevilla Vincenzo Montella ya yi barkwancin cewa kila sai sun daure Alexis Sanchez domin ganin dan wasan na gaba na Manchester United bai yi musu illa ba a karawar zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16, da za su yi Larabar nan.

Sanchez mai shekara 29 ya ci bal sau daya ne kawai a wasa biyar da ya yi tun lokacin da ya koma Manchester United a watan Janairu.

Da kociyan yake magana a kan tsohon dan wasan na kungiyar Udinese da Barcelona da kuma Arsenal, Montella ya kara da cewa :" Na san shi sosai tun lokacin da yake wasa a Italiya.''

Ya ce ya gyaru sosai, kuma yana ganin Manchester United tana da dan gaba mai gudun tsiya, wanda kila sai sun sa kwado sun kulle shi ko kuma su sa igiya su daure shi.

Wannan shi ne karon farko da United ta kai matakin sili-daya-kwale a gasar ta zakarun Turai tun 2014, yayin da ita kuwa Sevilla ba ta taba kaiwa wasan dab da na kusa da karshe ba, bayan da Leicester ta doke ta a bara.

Wasan da za a yi a filin Estadio Ramon Sanchez Pizjuan shi ne na biyu da kociyan dan Italiya zai taba jagoranta a gasar cin kofin zarun Turai.

Shi kuwa takwaransa na United Jose Mourinho ya jagoranci wasa 139 a gasar, kuma ya ci kofin sau biyu.