Za mu ba wa Barcelona mamaki - Antonio Conte

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Antonio Conte ya ce za su ba wa Barcelona mamaki a Nou Camp, a wasansu na biyu na zakarun Turai

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya ce za su yi kokarin yin wani abin mamaki ta hanyar fitar da Barcelona daga gasar kofin zakarun Turai bayan kunnen doki, 1-1 da suka tashi a karon farko ranar Talata a Stamford Bridge.

Conte ya ce suna dab da kammala wasa yadda ya kamata, daidai wa daida, sai suka gamu da sammatsin yin kuskure daya, kawai sai kuma abin takaici labari ya sha bamban.

Kociyan dan Italiya ya ce, sun yi kuskure daya, wanda kuma sun san cewa idan kana karawa da 'yan wasa irin su Messi da Iniesta da Suarez, muddin ka yi kuskure to za ka illar hakan.

Willian ne ya fara ci wa Chelsea kafin daga bisani ana minti 15 a tashi Lionel Messi ya farke wa Barcelona, aka tashi kunnen doki 1-1.

Barcelona wadda ke jagorantar teburin La Liga da tazarar maki bakwai, ba kasafai ta kai wasu hare-hare masu hadari ba, kafin ta farke.

A ranar Laraba 14 ga watan Maris za su yi karo na biyu na wasan a gidan Barcelona, Nou Camp.

Chelsea ta yi wasanta na karshe a can a kakar 2011-12, kuma duk da alkalin wasa ya kori John Terry a kashin farko na wasan, sun yi canjaras 2-2, inda suka fitar da Barcelona da jumullar kwallo 3-2, a wasan na kusa da karshe.

Daga nan ne kuma Chelsea ta samu nasarar doke Bayern Munich a wasan karshe da bugun fanareti ta dauki kofin.