Serena Williams: Na kusa mutuwa lokacin haihuwa

Serena Williams Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Serena Williams ce 'yar wasan tennis da ta fi samun nasara a wannan zamanin, inda ta ci kofunan manyan gasa 23

Tsohuwar gwana lamba daya a duniya ta wasan tennis Serena Williams ta ce kiris da ta yi sallama da duniya a lokacin haihuwar 'yarta Alexis Olympia Ohanian Jr a watan Satumba.

Ba'amurkiyar mai shekara 36, ta dawo fagen gasar kwallon tennis din ne a farkon watan nan na Fabrairu, a lokacin da ta hadu da yayarta Venus Williams suka wakilci Amurka a gasar kofin duniya na Fed Cup.

Sai dai gwanar wadda ta dauki kofin manyar gasar tennis 23 a wata kasida da ta rubuta wa CNN ta bayyana cewa, haihuwar da ta yi ta jawo mata matsaloli na lafiya. Ta ce ta ma yi sa'a da ta tsira da ranta.

Serena ta ce an yi mata tiyata ne aka cire mata 'yar bayan da bugun zuciyarta ya ragu kwarai a lokacin nakudar,

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Serena na kallon wani wasa na gasar Fed Cup a farkon watan nan tare da 'yarta Alexis Olympia Ohanian Jr

Sannan kuma ta ce abin da ya biyo baya sa'a 24 bayan haihuwar, kwanaki shida ne na rashin tabbas, kafa daya a duniya daya kuma a barzahu.

Bayan haihuwar sai da ta shafe mako shida a gadon jinya