Kofin Europa: Wenger zai hutar da manyan 'yan wasa

Dan wasan Ostersunds Saman Ghoddos (a tsakiyacentre) da Mesut Ozil Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mesut Ozil ba zai buga wasansu na biyu da Ostersunds sabo da rashin lafiya

'Yan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey da Mesut Ozil ba za su yi wasa na biyu na kofin Turai na Europa matakin kungiyoyi 32, da Ostersunds FK ranar Alhamis.

A karawarsu ta farko a Sweden kociyan kungiyar Arsene Wenger ya tafi da kusan cikakkiyar tawagar 'yan wasansa, inda suka ci wasan 3-0, amma yanzu zai yi amfani da wasu daga cikin matasan 'yan wasansa a Emirates.

Wenger ya ce, Ozil mai shekara 29 ba shi da lafiya, haka shi ma Ramsey yana murmurewa ne daga ciwon matse-matsi, amma ya ce hakan ba yana nufin zai yi wasarere ba ne da wasan.

Amma kociyan ya ce da Ozil kalau yake to da lalle zai sa shi, dangane da Ramsey kuwa, ya ce, duk da cewa dan Wales din mai shekara 27 ba zai yi wasan na Alhamis ba, ba zai kawar da yuwuwar sa shi a wasan karshe na ranar Lahadi na cin kofin Carabao ba.

Arsenal tana ta shida ne a teburin Premier, maki takwas tsakaninta da ta hudu Chelsea, kuma tana bukatar ta kammala kakar a cikin kungiyoyi hudu na gaba, ko kuma ta ci kofin Europa kafin ta samu damar shiga gasar zakarun Turai ta gaba.