Zakarun Turai: De Gea ya ceci Man United

David de Gea ya kade wani hari da 'yan Sevilla suka kai wa Man United

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Zuwa yanzu a wasa 19 ba a zura wa David de Gea bal a raga ba. Bai taba kaiwa wasa 20 ba da ba a zura masa bal a raga ba a kaka daya a Manchester United

Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea ya ceci kungiyar tasa ta yi canjaras ba ci a gidan Sevilla, a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin zakarun Turai, a ranar Larabar nan.

Golan na Spaniya ya rike kade miyagun hare-haren da 'yan wasan Sevilla Joaquin Correa da Steven N'Zonzi da kuma Luis Muriel suka kai.

United wadda wannan ne wasanta na farko a matakin sili-daya-kwale na gasar ta zarun Turai a cikin shekara hudu, ba ta kai wasu hare-hare masu yawa ba, kamar wanda Lukaku ya barar tun da farko da kuma na Rashford an kusa tashi.

Paul Pogba ya shigo wasan daga baya a minti na 17 lokacin da aka sauya Ander Herrera wanda ya ji rauni.

'Yan Sevilla da suka kai hare-hare 25 ba su ji dadin wasan ba, saboda yadda De Gea ya hana su ci da kuma barar da damarsu da suka yi.

Manchester United za ta fi jin dadin yadda wasan ya kare, yadda za ta karbi bakuncin karo na biyu a Old Trafford ranar talata 13 ga watan maris, inda suka yi nasara a wasa 15 daga cikin 18 a gidansu.

Wasan Shakhtar Donetsk da Roma;

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Golan Roma dan Brazil Alisson Becker ya kasa tare bugun tazarar da Fred ya yi

Golan Roma dan Brazil Alisson Becker ya kasa tare bugun tazarar da Fred ya yi

A daya wasan na kofin na zakarun na Turai na Laraba Shakhtar Donetsk ta farfado daga baya ta doke Roma da ci 2-1.

Dan wasan gaba na Argentine Facundo Ferreyra, wanda bai yi wasan ko da minti daya ba a zaman aro da ya yi a Newcastle a kakar 2014-15, shi ne ya farke wa Shakhtar bal din da dan wasan Roma dan Turkiyya Cengiz Under ya fara ci.

Daga nan ne kuma sai dan wasan tsakiya dan Brazil Fred mai shekara 24 ya sheko wata bal daga bugun tazara wadda ba ta zame ko ina ba sai cikin ragar bakin, Roma.