Jose Mourinho: Kila raunin Marcos Rojo ya yi muni

Ander Herrera lokacin da ya ji rauni a wasan Sevilla Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daman Ander Herrera ya dawo daga jinya ne bayan rasa wasansu da Newcastle da Huddersfield

Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce kila raunin da Ander Herrera ya ji a wasansu na jiya Laraba na kofin zakarun Turai da suka yi canjaras ba ci da Sevilla, ya yi tsanani.

Dan wasan tsakiyar na Spaniya ya ji ciwon ne minti 17 da shiga fili a karawar ta farko ta matakin kungiyoyi 16, abin da ya sa United ta maye gurbinsa da Paul Pogba.

Daman Herrera ya dawo daga jinya ne bayan da ya rasa damar buga wasanninsu a watan Fabrairu da Newcastle da kuma Huddersfield.

Kociyansu Jose Mourinho ya ce daman kamar dan wasan bai warke ba sarai, amma likitoci suka ce ya samu lafiya dari bisa dari, kuma zai iya wasansu da Huddersfield na kofin FA, ranar Asabar da ta wuce.

Manchester United daman ta rasa 'yan wasanta na baya Phil Jones da Marcos Rojo, da na tsakiya Marouane Fellaini da dan gaba Zlatan Ibrahimovic wadanda duk suke jinya.