Mai kungiyar Sunderland zai bayar ta ita kyau

Mai kungiyar Sunderland Ellis Short Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A kakar da ta wuce ne Sunderland ta fadi daga gasar Premier

Attajirin da ya mallaki Sunderland Ellis Short ya ce zai bayar da ita kyauta idan har wanda zai saye ta zai yarda ya karbe ta da dimbin bashin da ke kanta.

Short ya ce duk da ya sa kungiyar ta gasar kasa da Premier, Championship, wadda kuma ke neman faduwa daga gasar a kasuwa har yanzu ya rasa wanda zai saye ta.

Rahotanni sun ce attajirin dan Amurka a da yana neman fam miliyan 50 ne na hannun jarinsa a kungiyar.

To amma kuma yanzu ya hakura da hakan, inda ya ce zai bayar da ita kyauta, muddin wanda zai karbe zai yarda ya gaji tarin bashin da ke kanta, wanda a shekara ta 2016 ya kai fam miliyan 137 da dubu 300.

Kungiyar ta gamu da faduwar daraja ne domin a lokacin da tana gasar Premier a 2016, attajirin ya sa mata farashin fam miliyan 170 ne ga duk mai so.