Daliban jami'ar Moscow sun yi korafi kan gasar Kofin Duniya

Takardar da daliban suka rika sanya hannu domin nuna goyon bayansu ga boren Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Daliban na Jami'ar Moscow State University sun rika sanya hannu a wata takardar intanet ta nuna kin amincewarsu da matakin hukumomin kasar

Dalibai a fitacciyar jami'ar Rasha suna murnar samun kwaryakwaryar nasara a kan shirinsu na yakar matakin hukumomin kasar na tilasta musu ficewa daga harabar makarantar a lokacin gasar cin kofin duniya ta shekarar nan.

Daliban sun nuna bacin ransu ne kan shirin kafa dandalin 'yan kallo a lokacin gasar a kusa da wuraren kwanansu, na jami'ar ta Moscow State University, inda za a girke manyan allunan majigi, wadanda mutane za su rika taruwa suna kallon wasannin na kofin duniya.

Wasu daliban ma har sai ta kai an tashe su daga dakunan kwanan nasu domin a ba wa jamia'n tsaro da za su tabbatar da doka da oda, a lokacin gasar wadda za a fara a watan Yuni har zuwa wata daya.

Sannan kuma wasu daliban da dama sun nuna bacin ransu saboda za a matsar da jarrabawarsu gaba zuwa watan Mayu, yayin da wasu kuma ke kukan za a takura musu ta yadda za su yi jarrabawa shida a kasa da mako biyu.

Sakamakon korafin daliban a yanzu hukumomin kasar ta Rasha, sun fitar da wata sanarwa, wadda a ciki suke tabbatarwa tare da yi wa daliban jami'ar ta Moscow alkawarin cewa, za a samarwa daliban da tagogin dakunan kwanansu ke kusa da inda za a girke majigin wuraren kwana na wucin-gadi.

Shi kuma shugaban makarantar ya fitar da tasa sanarwar wadda a ciki yake sheda wa daliban da aka so sauya lokacin jarrabawarsu cewa za a dawo da ita ainahin lokacin da aka tsara tun da farko.