Za a 'haramta wa Samir Nasri buga kwallon wata shida'

Samir Nasri Hakkin mallakar hoto Twitter

Tsohon dan wasan Manchester City Samir Nasri na fuskantar haramcin buga kwalo tsawon wata shida da aka same shi da laifin yin karin ruwan da ya keta dokokin hukumar a wani asibitin Los Angeles a 2016, a cewar lauyansa.

An yi wa Nasri, mai shekara 30, karin ruwan ne a lokacin da yake hutu, sai dai hakan ya saba dokar hukumar hana shan abubuwan kara kuzari, lamarin da ya sa hukumar da ke Spain ta bincike shi.

Lauyan Nasri ya shaida wa BBC Sport cewa Uefa ce da kanta za ta yi masa wannan haramcin.

BBC Sport ta tuntubi Uefa domin jin karin bayani.

Rahotanni a Spain sun ce za a sanar da hukuncin da aka yanke wa dan wasan ranar Litinin.

Wani kamfani mai zaman kansa na likitoci mai suna Drip Doctors ya yi wa Nasri, wanda ba shi da kulob din da yake buga wa kwallo tun bayan barinsa Antalyaspor na kasar Turkiya a watan Janairu, karin ruwan a otal dinsa.

A wancan lokacin, Manchester City ta bai wa Sevilla aron dan wasan kuma hoton da ya dauka da daya daga cikin shugabannin kamfanin Jamila Sozahdah ya jawo ce-ce-ku-ce.

Labarai masu alaka