Manchester United ta doke Chelsea 2-1

Jesse Lingard lokacin da yake cin Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jesse Lingard ya ci bal dinsa ta 13 a bana, bayan da ya shigo wasan daga baya

Manchester United ta sake komawa matsayi na biyu a teburin Premier bayan da Jesse Lingard wanda ya shigo daga baya ya ci musu bal din da ta sa suka doke Chelsea 2-1 a Old Trafford.

Willian ne ya fara sa Chelsea a gaba tun kafin tafiya hutun rabin lokaci ana minti 32 da fara wasa, sai dai minti bakwai tsakani sai Romelu Lukaku ya rama wa United.

Wasa ya yi nisa ana minti 75 sai Lukakun wanda ya ci tsohuwar kungiyar tasa, ya aika wa Lingard wata bal daga bangaren dama, shi kuwa bai yi wata-wata ba , ya ci da ka, bayan nan ne kuma Alvaro Morata ya ci wa Chelsea bal din da za ta zama an yi 2-2, amma bisa kuskure aka haramta ta da cewa an yi satar gida.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne karon farko a wasa takwas da Lukalu ya ci tsohuwar kungiyar

Saboda wasa daya kawai da ta ci daga cikin hudu da suka wuce a gasar ta Premier hadi kuma da wasa goma da Tottenham ta yi ba tare da an doke ta ba, hakan ya sa Chelsea yanzu ta fice daga cikin kungiyoyi hudu da ke gaba-gaba, inda ta zama ta biyar, yayin da ya rage saura wasa goma a kammala gasar.

Manchester City wadda ke da kwantan wasa daya tana nan kan gaba da maki 72, sai kuma United wadda ta dawo ta biyu yanzu bayan Liverpool ta dan rike matsayin, tana da maki 59 a wasa 28.

Liverpool tana ta uku a wasa 28, da maki 57, yayin da Tottenham take matsayi na hudu da maki 55, Chelsea ta zama ta biyar da maki 53 a wasa 28. West Brom ce ta karshe lamba 20 a teburin na gasar ta Premier.

Chelsea za ta sake komawa birnin na Manchester a lokacin da za ta fafata da a Etihad da Man City ranar Lahadi, 4 ga watan Maris da karfe 5:00 agogon Najeriya da Nijar.

Ita kuwa United sai washegarin ranar (Litinin 5 ga watan Maris) za ta je gidan Crystal Palace, Selhurst Park, inda za su fara taka leda da karfe 9:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.