Ina mamakin kaina da yawan cin kwallo - Harry Kane

Harry Kane lokacin da ya ci Crystal Palace Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harry Kane ya ci kwallo 14 a wasan Premier 13 da ya yi a watan Fabrairu

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane ya ce ya ba wa kansa da kansa mamaki yadda cikin sauri a bana ya ci yawan kwallon da ya ci a bara, bayan da ya ci bal din da a kusan karshen tashi suka doke Crystal Palace, wadda ke cikin hadarin faduwa daga Premier, 1-0.

Kane ya zura kwallo a raga sau 35 a wasa 38 a kakar da ta wuce ta 2016-17, kuma a bana ya yi wannan bajinta a wasansa na 36 a ranar Lahadin nan, lokacin da ya ci West ham da ka a minti na 88.

Da farko ana ganin kamar Tottenham za ta kasa cin moriyar kankane wasan da ta yi da kashi 76 cikin dari, inda dan wasan na Ingila ya barar da damar da ya samu ta kurkusa a farkon dukkanin kashi biyu na wasan.

Kane mai shekara 24, ya ce shi ya san yana kan kwazonsa, wanda hakan ke ba shi kwarin guiwa a duk lokacin da za su shiga fili.

Dan wasan yanzu ya sake dawowa kan matsayinsa na wanda ya fi cin bal a gasar Premier, da bal ta 24 da ya ci a kakar nan, ya zarta Mohamed Salah na Liverpool.

Kungiyar ta kociya Mauricio Pochettino ita ce daya da har yanzu ba a doke ta ba a gasar Premier a wannan shekara ta 2018, ko da yake wannan ce kuma nasara ta uku a wasansu goma na baya bayan nan