Manchester City: Guardiola zai ci gaba da sanya zirin kyalle

Manchester City boss Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guardiola ya sanya ruwan dorawar kyallen a wasan karshe na cin kofin Carabao

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce zai ci gaba da sanya zirin kyalle ruwan dorawa abin da ya sanya hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhume shi da karya dokar tallata wata manufa.

Guardiola ya ce ya sanya kyallen ne - wanda ake ganinsa tamkar wani sakon siyasa ne - domin nuna goyon bayan 'yan adawar Catalonia da aka daure.

"Ni dan adam ne kafin na zama koci," in ji dan kasar ta Spain mai shekara 47.

"Su (jami'an FA) sun san cewa zan rika sanya ruwan dorawar kyallen nan a ko da yaushe."

Tsohon kocin na Barcelona ya kara da cewa: "Ban yi haka domin siyasa be, na yi ne domin dimokradiyya: na yi ne domin na taimaka wa mutanen da aka gallazawa ba tare da sun yi laifin komai ba."

An ba shi zuwa karfe shida na yammacin ranar Litinin, biyar ga watan Maris domin ya ba da amsa kan tuhumar da FA ke yi masa.

FA ta tattauna da Guardiola a kan batun a tsakiyar watan Disamba sannan ta yi masa gargadi kan ya daina sanya kyallen sau biyu amma bai daina ba.

Daga nan ne aka tuhume shi, lokacin da ya ake sanya kyallen a cikin filin wasa - a karawar da Wigan ta doke City ranar Litinin.

Labarai masu alaka