'Ba za a yi amfani da fasahar bidiyo mai taimaka wa lafiri ba a gasar Zakarun Turai'

Fasahar amfani da bidiyon taimaka wa alkalin wasa

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, Aleksander Ceferin ya ce yana goyon bayan amfani da fasahar, amma ba ya so a yi gaggawa

Ba za a yi amfani da fasahar bidiyo mai taimaka wa alakalin wasa warware takaddama ba a gasar cin kofin zakarun Turai saboda akwai alamun rudani da yawa in ji shugaban Uefa.

Hukumar gudanarwar kwallon kafa ta duniya wadda ke yanke hukunci kan dokokin wasan za ta gana ranar Asabar domin yanke hukunci ko za ta amince da amfani da fasahar dindindin.

Idan hukumar ta amince to ya zama dole ke nan hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta yi amfani da fasahar a gasar cin Kofin Duniya.

To amma kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, Aleksander Ceferin ya ce: ''A ko da yaushe 'yan kallo na ganin allon talabijin na fasahar, amma kuma ba wanda ya san yadda take aiki.''

Ya kuma kara da cewa, ba za su yi amfani da ita ba a gasar cin kofin Zakarun Turai a kaka mai zuwa ba.

Ya ce shi dai a wurinsa za ta iya kasancewa fasaha mai kyau, amma bai kamata a gaggauta amfani da ita ba.

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Kofin FA: An yi amfani da fasahar wajen hana bal din da mata ya ci Huddersfield a wasan cin kofin FA zagaye na biyar

An yi gwajin amfani da fasahar a wasu wasannin cin kofin FA a Ingila. Sannan an yi amfani da ita a gasar kofin Carabao, inda aka yi amfani da ita a wasan karshe na gasar ranar Lahadi, har ma kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya nuna rashin jin dadinsa kasancewar ba ta hana bal ta biyu da Manchester City ta ci su ba.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino a ranar Litinin ya ce yana ci gaba da bayar da goyon bayan ganin an yi amfani da fasahar a gasar cin kofin duniya da za a yi a wannan shekarar.