'Yan wasan Arsenal ba su da kishi - Ian Wright

'Yan wasan Arsenal bayan da Man City ta doke su 3-0 a wasan karshe na kofin(Carabao) League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba wata kungiyar Premier da ta taba cin wata ta gasar da yawan kwallo har 3-0 a wasan karshe na gasar ta kofin League tun 2006

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Ian Wright ya ce 'yan wasan kungiyar ba su nuna kwazo da kishi ba a fafatawar karshe da suka yi ta cin kofin Carabao wanda Manchester City ta casa su 3-0, ranar Lahadi.

Wright wanda ya ci wa Arsenal bal 185, ya ce sam-sam 'yan wasan ba su yi komai ba, wasan da suka yi lami ne kawai.

Ya kara da cewa kowa ya riga ya gane cewa magana ce ta jagoranci da kishi, kuma Arsenal ba ta da su.

Tsohon dan wasan na Arsenal ya ce, daman an san cewa haduwa da Manchester City ba abu ne mai sauki ba, saboda kungiya ce da take kokari a duk kakar nan, amma kuma abin takaici ne yadda Arsenal ta yi wasan.

Ya ce wasan karshe ne amma wai sai ka ga dan wasa yana tafiya kawai. Ai ba za ka so ka ga kungiyar da kake goyon baya tana wasa haka ba ba wani kuzari.

Sanna ya ce: ''Koma me muka fada a kan Alexis Sanchez da yadda yake a dakin sa jesi, ya ga cewa ba shi da ta yi dole ne ya tafi, saboda shi yana son ya yi nasara ne, ya kasance tare da mutanen da suke son yin nasara.''

Arsenal wadda maki 27 ne tsakaninta da jagorar Premier Manchestrer City, za ta kara da AC Milan a wasan matakin kungiyoyi 16 na gasar Europa a watan Maris.

An doke kungiyar ne ta Arsene Wenger a karawar ta Wembley, inda Pep Guardiola ya dauki kofinsa na farko a matsayin kociyan Manchester City.