Kwallon Kwando: Najeriya ta kama hanyar gasar duniya

Wani dan wasan kwando na Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Najeriya ta yi nasara a dukkanin wasanninta na karon farko a rukuninta

Tawagar 'yan wasan kwallon kwando na Najeriya maza, kamar yadda aka yi tsammani ta yi nasarar tsallake wasannin karon farko na rukuni na biyu, Group B, na neman gurbin gasar kofin duniya ta 2019, ba tare da an ci ta ba.

'Yan Najeriyar sun doke Uganda suka yi awon gaba da Rwanda kana kuma suka casakara mai masaukin baki Mali, da akasari bambancin kwallo 33.

A wasannin rukuni na hudu, Group D, wadanda aka yi a babban birnin Mozambique, Maputo, mai masukin baki Mozambique da Senegal su ne suka zama gaba a rukunin, inda kowacce daga cikinsu ta yi nasara sau biyu aka kuma doke su sau daidai.

Zakarun Afrika Tunisia sun gama wasansu na rukuni na daya Group A ba tare da an doke su ko sau daya ba.

Kamar yadda su ma 'yan Angola suka kammala wasan nasu na rukuni na biyu, Group B ba tare da an cinye su ko sau daya ba, dukkanin rukunan biyu sun yi wasanninsu na zagayen farko ne a watan Nuwamba.

Yanzu sai a watan Yuni da na Yuli za a yi zagaye na gaba na neman gurbin zuwa gasar ta cin kofin duniya na kwallon kwandon, inda ake da gurbi biyar daga Afirka, a gasar da za a yi a karon farko da kasashe 32 a China a watan Agusta.