'Antonio Conte ne ya fi dacewa da kociyan Italiya'

Antonio Conte

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Antonio Conte ya yi kociyan Italiya daga 2014 zuwa 2016

Kociyan Chelsea Antonio Conte shi ne ya fi dacewa da zama kociyan tawagar 'yan wasan Italiya na gaba in ji mataimakin kwamishina a hukumar kwallon kafa na kasar, Alessandro Costacurta.

Conte ya horad da tawagar ta Italiya wadda ake wa lakabi da Azzurri daga shekara ta 2014-2016 kafin ya tafi Chelsea, inda ya ci kofin Premier a shekararsa ta farko.

Babban jami'in ya ce kawo yanzu bai zabi wanda za a ba aikin ba, amma yana ganin Conte shi ne wanda zai fi dacewa, kamar yadda ya bayyana a jaridar labaran wasanni ta Italiya, Gazzetta dello Sport.

Jaridar ta ce jami'in yana kuma duba yuwuwar daukar tsohon kociyan Manchester City Roberto Mancini da tsohon kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti da kuma tsohon kociyan Leicester Claudio Ranieri.

Costacurta ya ce lalle kam ba shakka zai yi magana da Conte nan da 'yan watanni, inda zai yi masa tayin aikin.

Yanzu Conte, mai shekara 48, yana da ragowar wata 18 a kwantiraginsa da Stamford Bridge (Chelsea).

Italiya dai ta kori kociyanta Giampiero Ventura a watan Nuwamba, bayan da ya kasa sama wa kasar gurbin gasar cin kofin duniya da za a yi a wannan shekara ta 2018 a Rasha.

Amma kuma tsohon dan wasan na AC Milan ya ce tuni Conte ya nuna ya san yadda zai rike kungiya ta kasa, yayin da sauran ba su nuna ba.