'Neymar na cike da burin wasan PSG da Real Madrid'

Neymar lokacin da ya ji raunin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ciwon da Neymar ya ji a idon sawu, bai yi tsananin da za a yi masa tiyata ba in ji kociyansu Unai Emery

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Neymar yana da 'yar karamar dama ne ta yin wasan karo na biyu na Zakarun Turai da Real Madrid ranar Talata mai zuwa.

Dan wasan na Brazil mai shekara 26 yana murmurewa ne daga raunin da ya ji a idon sawu a lokacin wasan da suka doke Marseille 1-0 ranar Lahadi.

Kociyan kungiyar ta PSG Unai Emery ya musanta rahotannin da ke cewa dan wasan mafi tsada a duniya yana bukatar a yi masa tiyata ne a kafar kan raunin da ya ji.

Kociyan ya ce Neymar yana son taka leda a kowa ne wasa kuma ya ci buri a kan wasan da za su sake da Real Madrid na kofin na Zakarun Turai, zagayen kungiyoyi 16.

To amma Emery ya ce abin takaicin shi ne dan wasan ba lalle ba ne ya samu yin wannan wasa saboda 'yar damar da yake da ita ba ta da yawa saboda raunin.

Dan wasan na gaba ya koma PSG ne a kan kudin da ba a taba sayen wani dan wasa ba, fam miliyan 200 daga Barcelona, a watan Agusta, kuma ya ci bal 29 a wasa 30.

PSG tana saman teburin gasar Faransa da tazarar maki 14 tsakaninta da mai bi mata baya Monaco, kuma a ranar 6 ga watan Maris za ta karbi bakuncin Real Madrid, wadda ta ci su 3-1 a wasan farko a Santiago Bernabéu.