Anya Harry Kane na son daukar kofi?

Harry kane Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harry Kane ya ci bal ta 150 a karshen makon da ya wuce

Kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya kafe cewa gwarzon dan wasansa na gaba Harry Kane yana jin dadin zama kuma zai iya daukar kofi a kungiyar.

Tsohon kociyan kungiyar Andre Villas-Boas, wanda aka kora a watan Disamba na 2013, ya ce dan wasan wanda yake kan gaba wajen cin bal a gasar Premier dole ne ya bar kungiyar in dai yana son ya dauki kofi.

To amma a martanin da ya mayar kan maganar kociyan kungiyar Pochettino ya ce dan wasan mai shekara 24, wanda ya ci bal 24 a Premier a shekarar nan yana jin dadin zamansa a kungiyar kuma ba shakka yana son daukar kofuna a kungiyar kamar kowa.

Ya ce suna kulob din ne domin su taimaka masa ya bunkasa har ya kai ga cimma buri ya dauki kofuna.

Kane, wanda a bara ya kawar da tarihin da Alan Shearer ya kafa na shekara 22, na dan wasan da ya fi cin kwallo a cikin shekara daya a Premier, yana kan hanyar kara cin kyautar dan bal din da ya fi ci kwallo ''Golden Boot'' a karo na uku a jere, kuma a yanzu yana gaban Mo Salah na Liverpool da bal daya.

Jumulla a kakar nan Kane ya ci bal 35 kuma ya kama hanyar cimma tarihin da Clive Allen ya kafa a Tottenham wanda ya ci kwallo 49 a kaka daya ta 1986-87.