Man City ba za ta yi sako-sako ba da matashi Phil Fode

Phil Foden

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kociyan Man City Pep Guardiola ya ce 'yan kallon da suka ga wasan Foden na farko a babbar kungiyar sun yi sa'a

Ga alama Manchester City na shirin kulla sabuwar yarjejeniya mai tsawo da matashin dan wasanta Phil Foden, wanda ya samu karbuwa sosai a wurin kociyansu Pep Guardiola, idan ya kai shekara 18 a watan Mayu.

Ba a dai fara magana a kan batun ba, amma bayan da kungiyar ta zuba makudan kudade a bangare matasan 'yan wasanta, City ta zaku ta rike gwanin matashin dan wasan nata.

A kakar nan Foden ya samu shiga cikin 'yan wasan da Pep Guardiola yake amfani da su, inda ya yi wasa har sau shida.

Foden wanda mai goyon bayan Manchester City ne tun yana dan karami, shi ne ya zama gwarzon dan wasan gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekara 17 wanda Ingila ta dauka a watan Oktoba, inda ya ci bal biyu a karawar karshe da Spaniya.

A watan Yuli an sa shi cikin tawagar Manchester City da ta je rangadin wasannin shirin tunkarar kakar bana a Amurka.