Ban zan damu ba sosai don na rasa aikina - Wenger

Arsene Wenger

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Wenger ya damu da yadda ake yawan tambayarsa kan ci gaba da zamansa a Arsenal

Arsene Wenger ya ce tsira da aikinsa na kociyan Arsenal ba wani abu ne da ya dame shi ba sosai, bayan da aka doke su a wasa shida daga cikin 12 a shekarar nan ta 2018.

A ranar Alhamis Gunners din za su kara da ta daya a tebur Manchester City a gasar ta Premier, kwana hudu bayan Cityn ta casa su 3-0 a wasan karshe na cin kofin Carabao a filin Wembley.

Maki 27 ne tsakanin Arsenal din da City a tebur, sannan kuma maki 10 tsakaninta da ta hudu Tottenham, a fafutukar neman gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta kaka ta gaba.

Wenger wanda yake aikin horad da Arsenal tun 1996, ya ce yana mamakin yadda har yanzu ake tambayarsa irin wadannan tambayoyi game da ci gaba da rike aikin nasa.

Kociyan dan Faransa mai shekara 68 ya kulla sabuwar yarjejeniyar shekara biyu a watan mayu na 2017, bayan da ya jagoranci kungiyar ta dauki kofin FA na uku a kaka hudu, ko da yake sun kasa samun gurbin gasar Zakarun Turai a karon farko a shekara 20.

Wenger ya ce babban abin da ya dame shi a yanzu shi ne ya ga ya shirya 'yan wasansa yadda za su tunkari wasan gobe, amma ba wai damuwa da matsayinsa ba.

Cin kofin Turai na Europa wata hanya ce da Arsenal za ta samu gurbin gasar Zakarun Turai, kuma za ta kara da AC Milan a matakin kungiyoyi 16 da za a tankade rabi zuwa wasan dab da na kusa da karshe.