Neymar zai yi jinyar akalla mako shida

Neymar lokacin da ya ji rauni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Neymar ya ci bal 29 a wasa 30 tun da ya je PSG

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Neymar zai yi jinyar akalla mako shida kuma ba zai yi wasansu na biyu da Real Madrid ba na Zakarun Turai, na ranar Talata in ji mahaifinsa.

Dan wasan na Brazil mai shekara 26, ya ji rauni ne a idon sawunsa a wasan da suka doke Marseille 1-0 na gasar Faransa ta Ligue 1, ranar Lahadi.

A ranar Talata kociyan PSG Unai Emery ya ce Neymar yana da 'yar karamar dama ta yin wasansu da Real, inda ya musanta rahotannin da ke cewa za a yi wa Neymar tiyata a kan raunin.

Kociyan ya ce ran Neymar ya dugunzuma saboda raunin domin yana son ya yi kowa ne wasa, musamman ma na Real Madrid wanda ya ci masa buri.

To amma a yanzu mahaifin dan wasan a wata hira da jaridar ESPN Brasil ya ce jinyar za ta dauki mako shida zuwa takwas ko da za a yi masa tiyata ko ba za a yi ba.

PSG ta ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 14 kuma a ranar 6 ga watan Mais za ta karbi bakuncin masu rike da kofin Zakarun Turai Real Madrid, wadanda suka ci su 3-1 a wasan farko na zagayen kungiyoyi 16.