An dage dakatarwar Rasha daga wasannin Olympic

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Rasha 168 ne suka shiga gasar ta huturu ta watan Fabrairu amma ba da sunan kasarsa

Kwamitin wasannin Olympics na duniya ya dawo wa da Rasha matsayinta na mamba a cikinsa bayan dakatar da kasar da aka yi daga wasannin Olympic na huturu da aka kammala a Pyeongchang ta Koriya ta Kudu ranar Lahadi.

Hukumar gasar ta Olympic ta haramta wa Rasha shiga gasar ta watan Fabrairu a kan laifin da aka samu hukumomin kasar da shi na hannu a ba wa 'yan wasansu abubuwan kara kuzari.

Tun kafin bikin rufe gasar a ranar Lahadi a Koriya ta Kudu, kwamitin na gasar ta Olympic ya ce za a dage dakatarwar, in dai ba a sake samun Rashar da saba ka'idar dokokin amfani da abubuwan kara kuzarin ba.

Dukkanin sauran gwajin da aka yi wa 'yan wasan Rasha a gasar ta Olympic, ba a same su da laifi ba, in ji kwamitin, wanda daga nan ne aka sanar da dage dakatarwar.

Shugaban kwamitin wasannin Olympic na Rasha Alexander Zhukov ya yi maraba da matakin na hukumar wasan Olympic din, IOC.