Za a yi wa Neymar tiyata

Neymar lokacin da ya ji rauni Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ya ci burin wasansu na biyu da Real Madrid, amma ba dama ya buga saboda raunin

Za a yi wa dan wasan Paris St-Germain na gaba Neymar tiyata a ranar Asabar kan raunin da ya ji a idon sawu a lokacin wasan da suka ci Marseille 1-0 a gasar Faransa ranar Lahadi.

Likitan tawagar kwallon Brazil Rodrigo Lasmar shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, kuma ya ce dan wasan mai shekara 26 ba zai yi wasa ba tsawon wata uku.

Ya ce Neymar ba zai iya samun damar yin sauran wasannin kungiyarsa PSG ba a kakar nan, amma yana sa ran zai warke ya yi wasannin gasar kofin duniya a watan Yuni.

Likitan ya ce za a yi wa Neymar aikin ne a wani asibiti da ke birnin Belo Horizonte na Brazil ranar Asabar da safe.

Da farko kociyan PSG Unai Emery ya ce Neymar yana da 'yar damar yin wasansu da Real Madrid na Zakarun Turai a mako mai zuwa, kafin kuma mahaifin dan wasan ya sanar cewa ba zai yi wasa ba tsawon wata shida zuwa takwas.

PSG ta ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 14 kuma a ranar 6 ga watan Mais za ta karbi bakuncin masu rike da kofin Zakarun Turai Real Madrid, wadanda suka ci su 3-1 a wasan farko na zagayen kungiyoyi 16.