Musuluncin Mohamed Salah na tasiri a kan magoya bayan Liverpool

Mohamed Salah na sujjadar godiya ga Allah bayan ya ci kwallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mohamed Salah na daga 'yan wasa Musulmi a Premier da ke nuna godiyarsu ga

Mesut Ozil da Mousa Dembele da Riyad Mahrez da Paul Pogba da kuma Mohamed Salah suna daga cikin 'yan wasa Musulmi da suke taka leda yanzu a gasar Premier.

Ana ganin yadda suke nuna alamar addinin nasu a filin kwallo, inda suke daga hannu suna addu'a kafin a fara wasa ko kuma su yi sujjada idan sun ci bal.

To amma Salah, wanda ya ci wa Liverpool kwallo 23 a Premier a kakar nan, addininsa ya yi tasiri sosai da har ya sa magoya bayan kungiyar suka sauya wata waka da ta yi fice a 1996 (Good Enough ta mawaki Dodgy).

An sauya amshin wakar ta yadda ya zamo na yaba wa da irin kokarin dan wasan gaban na Masar, inda masu rera ta ke cewa su ma suna son zama Musulmi, su ma suna son su zauna a Masallaci.

Wani hoton bidiyon magoya bayan kungiyar wanda aka sa a intanet a lokacin da suke rera wakar ya watsu sosai, har ta kai ma wadanda ba magoya bayan Liverpool ba ne suka manta da bambanci, suka yaba da bidiyon da wakar.

Kamar Salah, dan wasan Jamus ma Mesut Ozil yana alfahari da addininsa har ma yana nuna hakan a filin wasa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mesut Ozil na addu'a kafin wasansu da Arsenal da Burnley a watan Janairu a 2017

An ruwaito shi yana cewa: ''Ni Musulmi ne, na yi imani da haka. Za ka ga kafin a fara wasa Ina addu'a kuma ina jin dadin kasancewata a kan wannan hanya. Tana ba ni karfi sosai.''