Sai da na tashi tsaye a Liverpool - Virgil van Dijk

Jurgen Klopp da Virgil van Dijk

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Klopp yana da kirki sosai, kuma abubuwan da yake koya mana za mu ci moriyarsu sosai a gaba in ji Van Dijk

Virgil van Dijk ya ce sai da ya tashi tsaye ya dage a lokacin da ya koma Liverpool a kan fam miliyan 75 a watan Janairu.

Tsohon dan wasan na baya na Celtic da Southampton mai shekara 26, ya ci wa Liverpool kwallo a wasansa na farko a karawar da suka yi a Anfield da Everton a gasar kofin FA.

Van Dijk ya ce sai da ya dage ya sauya zuwa salon wasan kociyansu Jurgen Klopp, na wasa ba kakkautawa da kuma matsa wa abokan karawa.

Dan wasan na Holland ya kara da cewa a nan kullum abubuwa sua da tsanani. Suna aiki tukuru, ga yawan gudu, a kwai bambanci sosai a nan. Da farko sai da na tashi tsaye kan yadda na saba wasa.

A kakar da ta wuce ne aka sa ran zai koma Liverpool bayan da ya gabatar da bukatarsa ta tafiya amma sai tafiyar ta gagara bayan da kungiyar ta Anfield ta bayar da hakuri a kan zargin da aka yi mata na zawarcin dan wasan ta bayan gida.

Wannan ne ya sa kociyansu a lokacin Mauricio Pellegrino ya fitar da shi daga cikin 'yan wasansa, sai ma shi kadai yake atisaye, tsawon wata takwas.

Sai a watan Satumba ya dawo da shi cikin 'yan wasansa sannan kuma a ranar daya ga watan Janairu komawarsa Liverpool ta tabbata, inda ya zama dan wasan bayan da ba a taba saye da tsada ba kamarsa.