Manchester City ta maimaita wa Arsenal 3-0

Sane ya daga ragar Arsenal

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Manchester City ita ce kungiya ta biyu a manyan gasannin Turai biyar da ta fi cin kwallo bayan Paris St-Germain

Manchester City ta cashe wa Arsenal a karo na biyu cikin kwana biyar inda ta sake lallasa su 3-0 ta kara tazarar da ta bayar a teburin Premier da maki 16.

Bayan da ta casa Gunners din 3-0 ta dauki kofin Carabao ranar Lahadi, City ta mamaye wasan a filin Emirates wanda ya kasance da 'yan kallo kusan rabi.

Bernardo Silva ne ya bude cin a minti na 15, Sai David Silva ya biyo baya a minti na 28, kafin kuma Sané ya ci cikammakin ta ukun minti biyar tsakanin.

Arsenal ta samu damar cin ladan-gabe da bugun fanareti amma Pierre-Emerick Aubameyang ya buga kai tsaye zuwa ga golan City Ederson, ya barar da damar.

Sakamakon ya sa Man City ta kara tsere wa Manchester United da ke ta biyu, kuma ya sa Pep Guardiola ya yi nasara a wasansa na 100 a kungiyar.

Ita kuwa Arsenal tana matsayi na shida a tebur, maki 10 tsakaninta da ta hudu, gurbin da akalla ya kamata ta kasance kafin ta samu damar zuwa gasar cin kofin Zakarun Turai ta gaba, ta hanyar Premier.

Ko da yake tana da wata damar ta hanyar kofin Europa idan har ta dauka.