Las Palmas ta rike Barcelona 1-1

Jonathan Calleri lokacin da ya ci Barcelona da fanareti Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jonathan Calleri ke nan lokacin da ya ci Barcelona da fanareti

Tsohon dan wasan West Ham na gaba Jonathan Calleri ya ci wa Las palmas fanaretin da ta sa ta rike jagorar La Liga, Barcelona da ci 1-1.

Sakamakon wanda ya sa Barcelona ta kuskure damar kara tazarar da ta ba wa Atletico Madrid wadda za su kara ranar Lahadi, daga maki bakwai zuwa biyar, duk da haka ya sa a yanzu ta yi wasa 33 ke nan a jere a gasar ba tare da an doke ta ba.

Lionel Messi ne ya ci masu masaukin nasu a minti na 21, da wani bugun tazara, wanda ya cilla bal din ta kere bangon da 'yan wasan Las Palmas suka yi, bal din da ba ta zame ko ina ba sai a cikin raga.

Amma kuma dawowa daga hutun rabin lokaci da minti uku kacal sai masu gidan suka samu fanareti Jonathan Calleri ya ci musu, har aka tashi kunnen doki 1-1. Las Palmas har yanzu tana cikin rukunin masu faduwa daga La Liga, inda take matsayi na 18 da maki 20 a wasa 26.

Atletico, wadda za ta kara da Barcelona ranar Lahadi a Nou Camp wasa takwas a jere tana yin nasara, kuma ita kadai ce a cikin kungiyo hudu na saman tebur da ta ci wasanta na La Liga a karawar tsakiya makon nan.

A sauran wasannin na La Liga da aka yi a ranar Alhamis da daddare;

Real Betis 0 - 0 Real Sociedad

Deportivo Alav├ęs 1 - 0 Levante