An daure mutanen da suka 'wulakanta shugaban Burundi'

Burundi President Pierre Nkurunziza Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption kotu tana cewa ana tuhumarsu da "laifin hada baki domin cin mutuncin shugaban kasa."

An daure jami'ai biyu a gidan kurkukun Burundi bayan an yi zargin cewa an wulakanta shugaban kasar a wani wasan kwallon kafa da ya shiga.

Jami'an ne suka hada wasan tsakanin kungiyar da Shugaba Pierre Nkurunziza ya murzawa leda da wata kungiyar 'yan hamayya.

Shugaban yakan yi tafiye-tafiye zuwa yankuna daban-daban na kasar tare da kungiyar kwallon kafarsa mai suna Haleluya FC.

Ranar uku ga watan Fabrairu ne kungiyarsa ta fafata da wata kungiya a garin Kiremba da ke arewacin kasar.

Bisa al'ada, akan sanar da kungiyar da za ta kara da ta shugaban kasar domin ta buga wasa a hankali ta yadda Shugaba Nkurunziza zai samu damar cin kwallo.

Amma a wasan da suka yi da Kiremba, kungiyar ta sanya 'yan gudun hijirar Congo cikin masu buga mata kwallo, wadanda ba su san cewa shugaban na cikin 'yan kwallon ba don haka ne "suka rika kai masa farmaki a duk lokacin da kwallo ta zo wurinsa har suka sa ya fadi sau da dama", a cewar wani ganau a hirarsa da kamfanin dillancin labaran AFP.

An daure mutumin da ya shirya wasan na Kiremba Cyriaque Nkezabahizi da mataimakinsa, Michel Mutama, ranar Alhamis, in ji AFP.

Kamfanin dillancin labaran ya ambato wata majiya a kotu tana cewa ana tuhumarsu da "laifin hada baki domin cin mutuncin shugaban kasa."

A shekarar 2017 wani rahoton majalisar dinkin duniya ya zargi Shugaba Nkurunziza da gwamnatinsa da laifin aikata laifukan keta hakkin dan adam.

Rahoton ya ce dakarun tsaro na gwamnati - da kuma mayakan sa-kai na 'yan adawa - sun kashe tare da gallazawa da kuma yin fyade bayan rikicin da ya barke a kasar a 2015.

An yi rikicin ne sakamakon shawarar da Nkurunziza ya yanke ta sake tsayawa takara karo na uku.

Ya yi nasara a zaben wanda 'yan hamayya suka kauracewa.

Labarai masu alaka