Brighton ta kara sa Wenger tsaka-mai-wuya da 2-1

Kyaftin din Brighton Lewis Dunk lokacin da ya ci Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kyaftin din Brighton Lewis Dunk ya ci bal dinsa ta farko a akakar nan a wasansu da Arsenal

A karon farko tun shekara ta 1982 Brighton ta doke Arsenal 2-1 ta kara sa kociyan Gunners Arsene Wenger a tsaka-mai-wuya.

Lewis Dunk ne ya fara daga ragar Arsenal minti bakwai da shiga fili, sannan kuma Murray ya kara ta biyu a minti na 26.

Arsenal ta ci dayarta ne ta hannun Pierre Emerick-Aubameyang ana saura minti biyu a tafi hutun rabin lokaci.

Arsenal ta mamaye kashi na biyu na wasan inda ana dab da tashi ta samu damar rama bal din amma Aubameyang ya kwarara bal din golan Brighton Mathew Ryan ya kama.

Kungiyar ta Arsene Wenger tana cikin yanayi na matsi inda a ranar Lahadi ta wancan makon Manchester City ta casa ta 3-0 ta dauki kofin Carabao, sannan kuma bayan kwana hudu ta sake maimaita mata 3-0 a wasan Premier.

Ana ganin cewa rashin nasara a hannun Manchester City wadda ke kan hanyar daukar kofin Premier a bana, idan ba wani abin mamaki da haushi ba ne, shan kashi a hannun kungiya kamar Brighton wadda ke kokarin tsira kar ta fadi daga Premier abin takaici ne ga magoya bayan Arsenal wadanda a kullum suke kosawa da Wenger.

Yanzu tazarar maki 13 ce tsakanin Arsenal ta shida, da Tottenham wadda take matsayi na hudu a teburin Premier, matakin da akalla ya kamata Gunners din su kai idan suna son zuwa gasar Zakarun Turai ta gaba.

Ko da yake kungiyar tana da damar zuwa gasar ta Turai ta hanyar kofin Europa idan ta dauka kamar yadda Manchester United ta yi a bara.

Wannan ne karon farko da Arsenal ta sha kashi a wasa hudu a jere tun watan Oktoba na shekara ta 2002, a wancan lokacin a hannun Everton da Auxerre da Blackburn da kuma Borussia Dortmund.