Dan wasan Italiya Davide Astori ya mutu

Davide Astori da bal a tsakiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Astori ya yi wa Fiorentina wasa 27 a kakar nan

Dan wasan tawagar Italiya kuma kyaftin din Fiorentina Davide Astori ya mutu yana da shekara 31 sakamakon gajeruwar jinya, abin da ya sa aka dage dukkanin wasannin gasar Serie A na Lahadi.

Kungiyarsa ce ta sanar a shafinta na Tweeter cewa dan wasan na baya ya mutu ne sanadin jinya da ta same shi kwatsam.

Da a ranar Lahadi da yamma Fiorentina za ta kara da Udinese a gasarsu ta Serie A amma kuma aka dage wasan da dukkanin sauran wasannin gasar na ranar saboda mutuwar.

Astori, wanda ya yi wa Italiya wasa sau 14 ya koma Fiorentina ne a shekarar 2016 daga Cagliari, kuma tun daga sannan ya taka musu leda sau 58.

"Fiorentina are profoundly shocked to have to announce the death of captain Davide Astori after a sudden illness," Fiorentina said.

Astori, wanda ya mutu ya bar matarsa da 'ya mai shekara biyu ya taso ne daga kungiyara matasa ta AC Milan kafin ta tafi Cagliari a 2008.

Ya yi shekara takwas a kungiyar sannan ya yi zaman aro a Roma da Fiorentina kafin daga bisani shekara biyu da ta wuce ya zauna dindindin a Fiorentina.