Barcelona ta yi fintinkau bayan doke Atletico 1-0

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Messi ne ya ci bal din daya tilo

Barcelona ta ci gaba da tafiyar-ruwa da take yi da kungiyoyi kan hanyarta ta daukar kofin La Liga a ranar Lahadi inda ta doke kungiya daya tilo da take binta ba kakkautawa Atletico Madrid 1-0 a Camp Nou.

Jagorar gasar ta La Liga ta mamaye wasan a kashin farko, inda Lionel Messi ya ci da wani bugun tazara a minti na 30, bal din da ta kasance ta 600 da ya ci a sana'arsa ta kwallon kafa. Amma bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci 'yan wasan Atletico kusan sun mamaye Barcelona sai dai sun kasa farkewa.

Yanzu Barcelona ta ci gaba da zama daram a kan tebur da maki 69 bayanwasan na mako na 27 da tazarar maki takwas tsakaninta da Atletico Madrid wadda ke da maki 61.

Sakamakon sauran wasannin La Liga na ranar Lahadi;

Levante1 - 1 Espanyol

Levante 1 - 1 Espanyol

Real Sociedad 2 - 1 Deportivo Alavés

Sakamakon gasar Bundesliga ta Jamus kuwa na Lahadi;

Köln 2 - 3 Stuttgart

Freiburg 0 - 4 Bayern München