Man City ta kara tazara bayan doke Chelsea 1-0

Bernardo Silva lokacin da ya ci Chelsea Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bernardo Silva ya ci bal biyu a wasan Premier biyu da ya yi wa Man City na karshen nan cikin wasa 25 da ya yi wa kungiyar gaba daya

Manchester City ta yi fintinkau a gasar Premier da tazarar maki 18 a kan tebur bayan da ta doke Chelsea da bal daya tilo wadda Bernardo Silva ya ci.

Silva, wanda yana daga cikin wadanda suka daga raga a wasan da City ta casa Arsenal 3-0 ranar Alhamis, ya ci bal din ne bayan da David Silva ya cillo masa ita cikin dakika 35 da dawowa hutun rabin lokaci.

'Yan wasan City sun mamaye karawar amma sai da suka yi hakuri kan yadda bakin nasu 'yan Chelsea suka tsare baya ba tare da wani kokari na kai hare-hare ba a wasan.

Kungiyar ta Antonio Conte ba wani hari kwakkwara da 'yan wasanta suka kai a tsawon fafatawar, sai kokarin kare gida kawai suka yi.

Yanzu an doke Chelsea a wasanta hudu daga cikin biyar na karshen nan na Premier da ta yi, kuma ta ci gaba da zama da tazarar maki biyar tsakaninta da ta hudu Tottenham, matsayin da akalla kowace kungiya ke fafutukar ba ta samu kasa da shi ba idan ta rasa kofin.