An fara bincike kan mutuwar Davide Astori

Davide Astori Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Astori ya yi wa Italiya wasa sau 14 kuma shi ne kyaftin din Fiorentina

Masu gabatar da kara sun fara gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar dan wasan Italiya kuma kyaftin din kungiyar Fiorentina Davide Astori.

Dan wasan na baya ya mutu ne ranar Lahadi yana da shekara 31 sakamakon rashin lafiya na lokaci daya.

Babban mai gabatar da kara na birnin Udine Antonio De Nicolo ya ce ya fara gudanar da bincike kan zargin kisan kai - wannan mataki ne da ake bi kafin gudanar da bincike kan gawa a Italiya.

Ya ce abu ne da ya wajaba a gudanar da bincike domin a tantance mutuwa ce ta gaskiya ko kuma wani yana da masaniya ko hannu a kanta.

Amma ya ce a yanzu dai ba wanda yake da hannu a kan komai.

Kungiyarsa Fiorentina ta ce a ranar Talata ne za a gudanar da bincike a kan gawar Astori kuma washegari, ranar Laraba a tafi da gawar zuwa Florence kafin a binne ta ranar Alhamis.

Astori, ya yi wa Italiya wasa sau 14, kafin ya koma Fiorentina a 2016 daga Cagliari, kuma ya taka wa kungiyar leda sau 58.

Ya mutu ya bar dadaddiyar abokiyar zamansa da 'ya 'yar shekara biyu.