Matsalar Arsenal: Mu ma muna da laifi - Koscielny

Arsene Wenger da daya daga cikin mataimakansa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cin da Brighton ta yi wa Arsenal 2-1 ya kara sa Wenger tsaka-mai-wuya

Dan bayan Arsenal Laurent Koscielny ya ce ba kociyansu Arsene Wenger kadai ya kamata a rika dora wa laifi ba kan halin da kungiyar take ciki a yanzu na rasa matsayi cikin hudun farko a teburin Premier.

Koscielny ya ce a matsayinmu na 'yan wasa muna da nauyin da ya rataya a wuyanmu a fili kuma muna bukatar mu hada kai. Abu ne mai wuya a ce laifinsa ne ko laifinmu ne.

Matsin lamba a kan Wenger ya karu bayan da Brighton ta doke su da ci 2-1 ya kasance maki 13 tsakaninsu da matsayi na hudu, wanda zai ba su damar zuwa gasar kofin Zakarun Turai ta gaba ta hanyar gasar Premier.

Wannan shi ne karon farko tun bayan shekara ta 2002 da Arsenal ta sha kashi a wasa hudu a jere.

Yanzu Arsenal ita ce ta shida a tebur da maki 45, yayin da ya rage wasa tara a kammala gasar ta bana.

Chelsea tana ta biyar da maki 53 sai Tottenham wadda ke matsayi na hudu kuma gurbi na karshe na samun tikitin gasar kofin Zakarun Turai, da maki 58.

Manchester United - wadda Litinin din nan za ta je wasa gidan Crystal Palace tana matsayi na uku da maki 59, sai kuma Liverpool wadda ke gabanta a matsayi na biyu da bambancin maki daya.