Na yi dabara ne kada Man City ta lallasa mu - Conte

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man City ta doke Chelsea 1-0: Antonio Conte ya ce Chelsea ba za ta iya fuskantar barazanar City ba

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya kare kansa a kan salon wasan da ya yi amfani da shi wanda jagorar Premier Manchester City ta doke su da ci 1-0.

Abin mamaki 'yan Chelsea ba kamar yadda aka san su ba su yi wani wasa na a-zo-a-gani ba a karawar, hatta ma wani dari ko da guda daya kwakkawara ba su kai ba a wasan da Bernardo Silva ya ci su kasa da minti daya da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kuma wannan bal daya tilo ita ce ta ba wa Manchester City damar bayar da tazarar maki 18 a teburin gasar ta Premier.

Wannan salon wasan ne wanda Chelsea ta yi amfani da shi ya sa mai sharhi a tashar wasanni ta Sky Sports Gary Neville ya kira salon da ''abin da ko alama ba za a lamunta da shi ba'' sannan ya zargi 'yan wasan na Conte da kasancewa kamar gumaka kawai a filin.

Haka shi ma abokin aikinsa a wannan tashar wasanni Jamie Redknapp ya bayyana salon na 'yan wasan Chelsea da cewa ;;abu ne da ya saba wa wasan kwallon kafa'' kuma ''babban laifi ga wasan kwallon kafa''.

Kociyan kungiyar dan Italiya ya mayar da martani kan sukan da cewa, ''dole ne ka ji ta bakin kowa ne mai suka, amma ni ba wawa ba ne da zan saki jiki na yi wasa da Manchester City, su ci mu 3-0 ko 4-0.

Ya ce a 'yan kwanakin da suka gabata Arsenal ta yi wasa da su sau biyu, sanna kuma kuna ta sukar Arsene Wenger saboda an ci Arsenal bal uku a cikin minti 30

Conte ya kara da cewa ya kamata mai sharhi ya yi amfani da tunaninsa idan yana maganar dabara, saboda ina ganin dole ne ka kasance kana da ilimin da ya kamata ka yi magana a kan dabara ba kawai ka saki baki kana magana kamar wani sakarai ko wawa ba.