Pep Guardiola ya amince da tuhumar FA

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Pep Guardiola yana sa alamar mai ruwan dorawa a rigarsa a matsayin goyon baya ga masu neman a ware na yankinsa na Kataloniya a Spaniya

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya amince da tuhumar da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta yi masa, a kan sanya wata alama ta sakon siyasa, ta dan zirin kwalle mai rawaya da yake sa wa a rigarsa a lokacin wasa.

Guardiolan daman yana da wa'adin zuwa karfe shida na yammar Litinin a agogon GMT ya amsa wa hukumar kan tuhumar, ta saba wa ka'idarta ta sanya tufafi da kuma talla.

A watan Nuwamba Guardiola ya ce ya sanya alamar ne domin nuna goyon bayansa ga 'yan awaren Kataloniya da hukumomin Spaniya ke tsare da su.

Tun da yanzu ya amince da tuhumar za a sanya wata rana a nan gaba domin zaman sauraren bahasi.

Hukumar kwallon kafar ta Ingila, FA, ta yi wa kociyan magana sau biyu a baya a game da sanya alamar a watan Disamba tare kuma da yi masa gargadi, amma ya bijire.

Yana da damar ya sanya alamar a wani wuri amma ba a filin wasa ba, kamar yadda ya sanya a lokacin wasansu na kofin FA na zagaye na biyar da Wigan ranar 19 ga watan Fabrairu da ya wuce.