Serene Williams na fama kan yadda za ta dawo wasa

Serena Williams
Image caption Burina shi ne jaririyata ta taso har ta rika kallona ina wasan tennis in ji Serena Williams

Tsohuwar gwana ta daya a duniya a tennis Serena Williams ta ce tana yawan tunanin yadda za ta iya ci gaba da wasa bayan da ta dawo atisaye sakamakon haihuwar 'yarta ta farko da ta yi.

A wannan makon ne Serena wadda ta ci manyan kofuna na gasar duniya 23 za ta dawo fagen gasar duniya a gasar da za a yi ta Indian Wells a California.

A wata hira da ta yi da BBC Ba'amurkiyar mai shekara 36 ta ce fatan da take na ganin jaririyarta 'yar wata shida ta taso tana kallonta a fili tana wasan na tennis shi ne yake kara mata kwarin guiwar ci gaba.

Ta ce; ''abu ne mai wuya. Akwai kwanaki da yawa, har ma yanzun nan, inda nake jin kamar 'ya zan iya ci gaba ne'?

" Abin da wahala, da matukar wahala amma na ci gaba kuma na san cewa ba lalle ina kan ganiyata ba ne, amma sannu a hankali ina dawowa, kuma kullum sabuwar rana ce kuma kullum ina samun ci gaba.''

"Tun da dai ina ci gaba, ko da kuwa ina yi ne kamar tafiyar kunkuru, to ba komai hakan ma ya yi min.''

A wata kasida da ta rubuta wa CNN a watan da ya wuce, Serena ta ce ta yi sa'a da ta rayu bayan da aka yi mata tiyata aka fitar mata da jaririyar tata Alexis Olympia saboda matsalar da ta samu lokacin haihuwarta.