Za mu iya doke Real Madrid ko ba Neymar - Alves

Neymar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ba zai sake wani wasa ba a kakar nan saboda jinyar da zai yi mai tsawo

Dan wasan baya na PSG Dani Alves ya ce duk da ba gwaninsu Neymar za su iya doke Real Madrid wadda ta ci su 3-1, a karawar farko, ta Zakarun Turai da suka yi.

Neymar ya tafi jinya ne har zuwa karshen kakar nan bayan da ya ji ciwo a idon kafarsa a wasan da suka doke Marseille 3-0 a makon da ya wuce a gasar Ligue 1.

Alves ya ce zabi biyu ne a gabansu a karawar ta ranar Talata, ko dai zauna su yi kuka, ko kuma su tashi su yi abin da ya wajaba su yi.

Dan wasan na Brazil ya kara da cewa da Neymar, PSG ta fi karfi, haka kuma ba Neymar ma muna da karfi saboda akwai sauran 'yan wasan.

Ya ce ba shakka za mu yi kewarsa. Amma magana ce ta tsakanin mu zauna mu yi kuka da kuma tashi tsaye mu ci gaba, kuma ko da yaushe zabi na biyu nake dauka.

A bana ba a taba doke PSG a gidanta Parc des Princes, ba a duk wata gasa, amma kuma ba ta taba galaba a kan Real Madrid ba a haduwarsu uku a baya a gasar ta Zakarun Turai.