Zakarun Turai: Real Madrid ta yi waje da PSG 5-2 jumulla

Cristiano Ronaldo lokacin da ya ci wa Real Madrid ta farko Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristiano Ronaldo ya ci wa Real Madrid kwallo 15 a wasa tara da ya yi wa kungiyar a karshen nan

Zakarun Turai Real Madrid sun kai wasan dab da na kusa da karshe na kofin na Turai bayan da suka bi jagora a gasar Faransa Paris St-Germain har gida suka casa ta 2-1, jumulla wasa gida da waje 5-2.

Cristiano Ronaldo wanda ya ci biyu a karawar farko wadda suka yi nasara da ci 3-1 a Madrid, shi ya fara daga raga ma a wannan karawa ta biyu a Parc des Princes, a minti na 51 da wasa inda ya ci da ka.

Alkalin wasa Felix Brych ya kori dan wasan tsakiya na PSG Marco Verratti a minti na 66 saboda laifi biyu da ya yi, na farko daman ya yi wa Casemiro keta, an ba shi katin gargadi, na biyu kuma ya bi lafirin da tsawa kan kin hura keta da yake gani an yi masa.

Bayan nan ne kuma suka yunkuro har kuma Edinson Cavani ya farke musu a minti na 71, bayan da bal din ta doki Casemiro sannan ta taba Edinson Cavani ta shiga raga.Bayan nan ne kuma suka yunkuro har kuma Edinson Cavani ya farke musu a minti na 71, bayan da bal din ta doki Casemiro sannan ta taba Edinson Cavani ta shiga raga.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption PSG ta samu cinta ne bayan da bal din ta taba Casemiro sannan ta taba Edinson Cavani ta shiga raga

Sai kuma a minti na 80 Casemiro ya ci wa Madrid ta biyu wadda ta zama ta karshe, ta karya bajintar PSG ta rashin doke su a gidansu a kakar nan gaba daya.

A wajen Zakarun na Faransa wadanda yanzu suka bayar da tazarar maki 14 a teburin gasar Ligue 1, wannan shi ne karo na biyu a jere da ake yin waje da su a gasar ta Zakarun Turai a matakin kungiyoyi 16.

Daman PSG ba ta taba galaba a kan Real Madrid ba a haduwarsu uku a baya a gasar ta Zakarun Turai.

Yanzu Real ta kai wasan dab da na kusa da karshe a karo na takwas a jere, inda kuma take kan hanyar daukar kofin sau uku a jere.