Zakarun Turai: Liverpool ta fitar da Porto da 5-0

Adam Lallana Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adam Lallana ya fara wasa a karon farko a cikin wata biyu

A karon farko tun 2009 Liverpool ta kai wasan dab da na kusa da karshe na Zakarun Turai bayan da suka tashi 0-0 a karawa ta biyu a Anfield, sakamakon da ya kasance 5-0 ke nan ta lallasa Porto gida da waje.

Sadio Mane ya kai kwararan hare-hare biyu, inda a guda daya sai da bal din ta doki turken raga, ya yi kararrawa, a kashin farko na wasan wanda kusan Liverpool ta mamaye.

Harin da Majeed Waris ya kai wa masu masaukin shi kadai ne wanda Porto ta kai na a-zo-a-gani.

Jurgen Klopp ya yi amfani da damar ya hutar da wasu daga cikin 'yan wasansa fitattu saboda karawar da Liverpool za ta yi ranar Asabar ta Premier da Manchester United (1:30 agogon Najeriya da Nijar).

Kociyan ya bayar da dama ga Joe Gomez da Adam Lallana domin su kara murmurewa bayan sun dawo daga jinya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool ta ci kofinta na Zakarun Turai na biyar a 2005 da bugun fanareti inda ta doke AC Milan

Liverpool za ta san wadda za ta hadu da ita a wasan na dab da na kusa da karshe idan aka fitar da jadawalin karawar ranar 16 ga watan nan na Maris da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya da Nijar.

Za a yi wasannin ne a makon farko da kuma na biyu na watan Afrilu.

Kila wannan wasan na Talata shi ne na karshe na kofin na Zakarun Turai na mai tsaron ragar Porto Iker Casillas mai shekara 36 - Kuma idan ya kasance haka to ya zama ya kasance da tarihin yin wasan gasar 167. Ana sa ran zai bar kungiyar ta Porto a karshen kakar nan, kuma ba a san inda zai koma ba.

Wasannin Laraba:

Tottenham Hotspur da Juventus (a karawar farko sun yi 2-2)

Manchester Cityda Basel (a karawar farko Manchester City ta ci 4-0)