Wariyar launi: 'Yan sandan Jamus sun karyata zargin Mo Farah

Sir Mo Farah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farah ya ce jami'in tsaron ya rika taba shi kamar wani mahaukaci, saboda bambancin launin fata

Hukumomin 'yan sandan Jamus sun ce sun kasa ganin wata alama ta cin zarafi na wariyar launin fata da aka yi wa Sir Mo Farah ba a filin jirgin sama na Munich.

Farah mai shekara 34, dan Birtaniya, amma asali kuma haifaffen Somalia yana kan hanyarsa ne ta tafiya Ethiopia domin shirya wa gasar gudu ta Landan da za a yi a wata mai zuwa, a lokacin da abin da ya yi zargi ya faru.

Dan gudun wanda sau hudu yana zama zakaran gasar Olympic ya sanya wani hoton bidiyo a shafinsa na Instagram wanda ke nuna sa-in-sa da aka yi da shi da wani jami'in tsaro a filin jirgin.

Hakkin mallakar hoto MO FARAH TWITTER
Image caption Shafin Instagram na Sir Mo Farah da hoton da ya sa

Sai dai a martanin da hukumomin 'yan sandan suka mayar, a wata sanarwa sun ce dan sandan bai yi wani laifi ba, kawai yana gudanar da aikinsa ne yadda ya kamata.

A rubutun da ya hada da hoton bidiyon na tsawon dakika 47, Sir Mo Farah, ya ce: ''Mutumin yana taba ni ne kamar wani mahaukaci. Wanda cin mutuci ne hakan karara. Abin takaici ne ka ga cin mutunci na wariyar launin fata a wannan rana da shekara. 2018...!!!!''

Sanarwar 'yan sandan na Jamus ta kara da cewa: ''Ga alama Sir Mo Farah bai lamunta da binciken matafiya da aka yi masa ba, kuma ya yi zargin danganta hakan da wariyar launin fata. Ba shakka ya harzuka sosai.''

A ranar Lahadi Farah ya ci gasar gudun da aka yi a Landan ta Big Half, gasa ta karshe da ya yi kafin babbar gasar ta Landan, wato London Marathon da za a yi ranar 22 ga watan Afrilu.